Hukumomin tsaro sun bayyana cewa yan ta’adda na Shirin Kaddamar da hare-hare a Kano

Spread the love

Gamayyar hukumomin tsaro a jihar Kano, sun gargadi mutane da su kaucewa wuraren cunkoson jama’a sakamakon Samun bayanan sirri kan yunkurin kawo hare-hare jihar da wasu yan ta’adda ke shirya wa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar Juma’a.

Sanarwar ta yi kira da a kauracewa dukkan wuraren taruwar jama’a zuwa Wani lokaci, don dakile wa da kuma bankado masu Yunkurin kawo hare-haren.

Sp Abdullahi Haruna ya kara da cewa don tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, an dauki duk shirin da yakamata na tsaro don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Haka zalika an baza jami’an tsaro na musamman wadanda suka kware wajen ganowa da kuma dakile aiyukan yan ta’adda.

Rundunar ta shawararci al’umma a duk lokacin da suka ga Wani Abu da ba su gamsu da shi ba , su gaggauta sanarwa a ofishin yan Sanda Mafi kusa don daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *