Hukumomin Tsaro Sun Bayyana Dalilinsu Na Hana Hawan Salla A Kano.

Spread the love

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron jihar sun sanar da dakatar da gudanar da bukukuwan hawan sallah karama.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori , ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar rundunar yan sandan dake unguwar Bompai a yau juma’a.

Kwamishinan yan sandan ya ce, a matsayin su na jami’an tsaro sun zauna tare da gwamnatin jihar Kano, inda suka basu shawarar cewa yin hawan sallar zai kawo matsaloli na rashin tsaro da kuma rasa rayuka da dukiyoyin jama’a, shi yasa suka dauki matakin hana yin hawan sallar baki daya.

CP Bakori  ya kara da cewa dukkan hawan sallah an dakatar da su kuma babu wanda za a bari ya hau doki yana yawo don yin kilisa.

Haka zalika ya shawarci iyaye da su jawa yayan kunne don su kaucewa dukkan wani abu da zai iya haddasa fitina, kuma duk wanda aka samu da makami zai fuskanci ba tare da bata lokaci ba.

Rundunar ta ce ta yi shirin ba wa kowa tsaro tare da tsare dukiyoyinsu a lokacin bukukuwan sallar da ma bayan ta.

Kwamishinan yan sandan ya ce an haramta fitowa da makami domin duk wanda aka kama za a  kama tare da gurfanar da shi a gaban kotu, don ya fuskanci hukunci.

Matakin rundunar ta ‘yansanda ya saɓa da aniyar da gwamnan jihar na Kano ya nuna na yin hawan, inda ya nemi dukkan masarautun Kano huɗu ƙarƙashin jagorancin Sarki Muhammadu Sanusi II da su shirya aiwatar da hawan.

Kazalika, shi ma Sarki Sanusi ya aika wa hukumomin tsaron jihar wasiƙa yana mai sanar da su shirinsa na gudanar da bikin al’adar da aka saba yi duk shekara.

Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta jam’iyyar NNPP mai adawa a Najeriya da masarautar Kano ba su ce komai ba game da batun.

Sanarwar haramcin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya sanar da soke shirinsa na yin hawan kamar yadda ya tsara tun farko, yayin da yake ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarki duk da matakin gwamnatin Kano na sauke shi.

A karshe Ibrahim Bakori, ya ce duk wanda yayi wani abu da ya saba da doka ba za su barshi ba ko waye domin a shirye hukumomin tsaron jihar suke a koda yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *