Hukuncin Kisa Ne Ya Dace Da Masu Kashe Jami’an Tsaro : Babangida Aliyu

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, ya buƙaci ake yanke wa duk wanda ya kashe jami’an tsaro, hukuncin kisa nan take.

Yayin da yake jawabi a bikin kammala karatun daliban makarantar Executive Intelligence Management Course (EIMC 17) a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NISS) a Abuja, Aliyu ya yi kira ga masu tsara dokoki su amince da wannan shawara domin rage yawaitar aikata laifukan kashe jami’an tsaro.

“Ban taɓa ganin wata ƙasa inda aka kashe sojoji 38 kuma mutane suka yi shiru ba,” in ji Aliyu.

“Ina bayar da shawara cewa duk wanda ya kashe jami’in tsaro shi ma s kashe shi ba ɓata lokaci.

“Soyayyar ƙasa tana bunƙasa ne idan gwamnati ta kare ‘yan ƙasa, kuma jami’an tsaro suna bukatar jin cewa suna da kariya don su yi aiki cikin kwanciyar hankali.”

Har ila yau, Aliyu ya soki gwamnoni kan yawan zargin Gwamnatin Tarayya game da matsalolin tsaro a jihohinsu.

Ya ce, “Gwamnoni su daina kuka da Gwamnatin Tarayya, su ɗauki nauyin tsaro a jihohinsu.

“Ana ba su maƙudan kuɗaɗe saboda tsaro, kuma ya kamata su tabbatar da cewa sun tallafa wa hukumomin tsaro yadda ya kamata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *