Hukuncin kotu: Yan Kasuwar Magani ta Sabongari a Kano sun rufe shagunansu bayan sun yi sallar Alkunut .

Spread the love

Yan kasuwar sayar da Magani ta Sabongari Kano, sun rufe shagunan su, har sai abunda hali ya yi, biyo bayan hukuncin wata babbar kotun tarayya a jahar Kano, inda ta umarce su, su tashi su koma Kasuwar Dangoro a karamar hukumar Kumbotso.

Sai dai yan kasuwar sun bayyana rashin jin dadin su kan hukuncin kotun, da cewar sun shirya dauka kara, kan yunkurin raba su da sana’arsu.

Shugaban yan kasuwar Maganin ta jahar Kano, Musbahu Yahaya Khalid, ya bayyana cewa sun samu kwafin hukuncin kotun da cewar kotun ta kori kararsu, inda lauyoyinsu suka shirya tsaf domin daukaka kara.

” korar kara ba sabon abu ba ne, mu na saran idan munje gaba za mu samu nasara”Musbahu”.

Kano: Wani mtukin Adaidaita sahu ya mayar wa da fasinjan sa wayoyin hannu Iphone 12 promax guda 3 da aka manta.

Gwamnati ta rufe katafaren shagon Sahad stores a Abuja

Musbaha Yahaya, ya ba wa marasa lafiya hakuri da cewar, lamarin ya faru ne badan suna so ba, domin sun sami labarin akwai wasu batagari da suke shirin far mu su shi yasa suka dauki matakin.

” Ma su sana’ar siyar da magani idan sun rasa sana’arnan ba mu san abunda za suje su yi ba”.

Ya kara da cewa, sun rufe kasuwar don gwamnatin ta san amfanin yan magani a jajar Kano.

” maganar da ake yi cewar yan Igbo ne ma su sana’ar magani wannan zance ne marasa tushe, zalinci ne, muna so al’ummar jahar manyan ta da kakana su sani an yi haka ne saboda zalinci.

Sai dai ya ce wajen da ake so a koma ba na gwamnati ba ne, kawai na wasu ne domin tsauwalawa yan kasuwar magani.

Haka zalika yan kasuwar maganin sun yi, sallah tare yin addu’o’in samun nasara a wajen Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *