Rundunar yan sandan jahar Kano ta bayyana cewa, ta shirya tsaf tare da sauran hukumomin tsaro , don bayar da cikakken tsaro gabanin yanke hukuncin kotun koli dama bayan sa.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel ne, ya bayyana hakan ta cikin wani faifan murya da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya raba wa manema labarai , a ranar Alhamis.
Kwamishina yan sandan ya ce , rundunar za su bayar da ingantaccen tsaro ga me da abunda ake tunkara , na hukuncin koli a ranar juma’a , ga me da zaben gwamnan jahar Kano.
“Hakika acan baya mun yi kowa ya gani , lokacin da aka yi zaben gwamna munga irin rawar da jama’a suka taka , munga kishin kasa, munga kishin jahar Kano, munga kishin kai yadda aka hada kai da mu ba a samu ya mutsi ba ko kadan” CP Gumel”.
Ya kara da cewa, bayan haka an tafi kotun sauraren kararrakin zabe da ta daukaka kara , wanda al’umma da Malamai , sarakuna da masu ruwa da tsaki suka bayar da goyon baya kan zaman lafiyar Kano.
” To wannan sakamako da za a bayyana na ranar juma’a , shi ne mataki na karshe kuma mu munsan mutanen jahar Kano mutane ne masu tsoron Allah duk abinda ya kawo za a karbe shi hannu bibiyu” Gumel.
Kwamishinan yan sandan ya ce tayar da tarzoma ba abinda ta ke haifar wa sai yada fitina , wasu su rasa rayukansu sannan kuma a sulwantar da dukiya tare da lalata sunan jahar Kano a idon duniya domin waje ne na kasuwanci da alfahari.
” Ba zamu yarda muna ji muna gani wani ya kawo son zuciya ko wata kungiya ayi amfani da wata dama a tayar da hargitsi a cutar da al’umma ba, mu yan sanda da sauran hukumomin tsaro a dunkule muke kuma a shirye muke , domin muna da mutane , kayan aiki da motoci da za su shiga lungu da sako mu tabbatar da tsaro”.
CP Gumel, ya yi kira ga al’ummar Kano karsu ji tsoro , ko firgitsa kan wani abu , sai dai ya ce duk lokacin da suka ga wani abu da ba su amince da shi ba , su yi gaggawar sanarwa da jami’an tsaron dan daukar matakin da ya dace.