ICC ta bayar da sammacin kama tsohon ministan tsaron Rasha

Spread the love

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC), ta bayar da sammacin kama tsohon ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu da kuma babban hafsan sojin ƙasar Valery Gerasimov.

Alkalan kotun sun ce ana zargin mutanen biyu da aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil adama a lokacin yaƙin Ukraine.

Ana zargin manyan jami’an sojin biyu da keta dokokin ƙasa da ƙasa ta hanyar kaddamar da hare-hare kan ababen more rayuwa na fararen hula da kuma gaza taka wa sojojin da ke karkashinsu birki.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kotun ke bayar da irin wannan sammaci kan jami’an gwamnatin Rasha, inda a watan Maris ɗin shekarar da ta gabata ta bayar da sammacin kama shugaba Vladimir Putin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *