Idan Aka Sauya Kashim Shettima A 2027 Mu Zamu Taka Farantin APC Kowa Ya Rasa : Matasan

Spread the love

Honarabul Aminu Abukakar Boyi , ya bayyana  cewa masu kulle-kullen sauya dan takarar mataimakin Shugaban kasa na jam’iyyar APC  a kakar zaben 2027 suna gaiyatowa APC faduwar zabe.

Honarabul Aminu Boyi na bayyana hakan ne alokacin da yake tsokaci bayan zargin sauya mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima  a 2027.

Boyi ya ce Kashim Shettima da Ahamed Bola Tunibu dan juma ne da dan jummai, don haka nasarar Jam’iyyar APC  ita ce tabbatar da takarar Tinubu tare da Kashim Shettima.

“Muna tabbatarwa da jam’iyyar APC  cewa matasa musamman ya kin arewa Kashim Shettima  ne fatansu, don haka duk wani yunkuri na sauya Kashim , matasan arewa za su taka farantin APC kowa ya rasa.

Ya kara da cewa Kashim Shettima  mutun ne na matasa kuma mai kishin yankin yankin arewa, wannan tasa matasa suka yanke hukuncin ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da ganin ba wanda ya yi gangancin taba kimar Kashim Shettima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *