Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan, ya yi rashin nasara a ƙarar da ya ɗaukaka kan hukuncin laifi da ya da ya sa aka garkame shi a gidan yari.
Wani alkali ya yi watsi da yunƙurin da Mista Khan da matarsa Bushra Bibi suka yi na soke hukuncin ɗaurin shekara bakwai da aka yanke musu kan karya dokokin aure na Musulunci.
An same su da laifi a watan Fabrairu na rashin ba da tazarar lokacin da ya dace tsakanin aurensu da kuma mutuwar auren Ms Bibi da tsohon mijinta.
Mista Khan ya shafe kusan shekara guda a gidan yari bisa wasu tuhume-tuhume da ake yi masa, waɗanda ya ce suna da alaƙa da siyasa, amma an dakatar da mafi yawa daga cikinsu bayan ya ɗaukaka ƙara.