Ina cika alƙawurran da na ɗauka – Tinubu

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana cika alƙawurran da ta yi wa jama’ar ƙasar.

Tinubu wanda ya taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 25 kan mulkin dimokuraɗiyya babu katsewa, ya kuma nemi haɗin kan al’umma domin samar da kyakkyawar ƙasa da za ta zamo abin alfahari ga ƴan baya.

Ya kuma yi gargaɗi a kan jefa dimokuraɗiyya cikin mawuyacin hali yana mai cewa “Dole mu ci gaba da haɗa kai wajen gina ƙasarmu da kuma jaddadawa a koda yaushe, cewa ba mu da wata ƙasa da ta fi Najeriya’’.

A wani jawabi da ya yi wa majalisar dokokin Najeriya, shugaba Tinubu ya nemi haɗin kan ƴan majalisar da ma sauran jama’ar ƙasar wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinsa da kuma bunƙasa Najeriya.

Shugaban Najeriyar ya kuma nemi goyon bayan majalisar wajen kammala aiki a kan kasafin kuɗin da ya gabatar mata, wanda ya ce zai taimaka wajen aiwatar da tsare-tsaren da gwamnati ke da su, masu muhimmanci ga jama’ar ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *