Ina godiya ga al’ummar Kano bisa addu’o’in da suka yi min – Abba Kabir

Spread the love

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya yi farin ciki maras misaltuwa da hukuncin kotun ƙolin da ya tabbatar da nasararsa a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Yayin da yake magana da manema labarai a harabar kotun jim-kaɗan bayan yanke hukuncin, gwamna Abba Kabir ya ce ya gode wa al’ummar jihar Kano da ma na Najeriya baki ɗaya bisa addu’o’in da suka shafe watanni suna yi masa.

A yau ne kotun ƙolin ƙasar ta tabbatar da nasarar Abba, inda ta soke hukuncin kotun ɗaukakka ƙara da ta ce Abba ba halastaccen ɗan jam’iyyar NNPP ba ne.

Tun da farko a cikin watan Satumba kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, inda ta ce Nasiru Gawuna na APC ne ya ci zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *