Ina Neman Afuwa Domin Ban Shirya Mutuwa Ba: Abba Dan-Kuda

Spread the love

Matashin nan da ake zargi da aikata laifin kisan Kai, ya bayyana jami’an Yan sandan jahar Kano, cewar bai Shirya Mutuwa ba.

Ana zargin Abba Garba ( Dan-Kuda) Mazaunin Unguwar Chiranci Dorayi Kano, da yin amfani da wukar Zarto , wajen yanka wuyan Zaharaddin Iliyasu, saboda sun samu sabani tun a Ranar 29 ga watan Maris 2024.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan sun samu rahoton faruwar lamarin Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tada dakarun Yan sanda karkashin jagorancin baturen Yan sandan Panshekara CSP Ya’u Sadik Abdul, tare bada umarnin rufe duk Wata hanya, da zata bayar da dama ga wadanda ake zargin.
Haka zalika sun yi gaggawar Kai matashin asibiti , inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Yan sandan sun yi nasarar Kama matashin lokacin da yake tattara kayansa a Unguwar Shahuci a birnin Kano, don  guduwa jamhuriyar Nijar.

Dan-Kuda ya tabbatar da cewa, shi ne ya dauki wuka ya yanka Abokin nasa, saboda ricikin da ya hada su.

ME YA HADA SU?

Wanda ake zargi Abba Dan-Kuda, ya bayyana cewa, marigayin ne ya yi masa fadan cewar baya yin azumi, inda ya tabbatar da cewa yana yi, daga nan Suka Fara har jami’an Yan suka Kama su tare da tafiya da su ofishinsu.

Bayan an samu daidaito ne ake zargin Dan-Kuda, ya lallaba, da wata wukar zarto ya yanka wuyan Zaharaddin,Wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

ME YASA DAN-KUDA YA CE BAI SHIRYA MUTUWA BA?

Sai dai Abba, ya ce bai Shirya Mutuwa ba, saboda bai san hakan zata kasance ba ga marigayin, sakamakon shan miyagun kwayoyi da yayi Kafin abun ya faru.

Ya Kara da ce yasha , Wiwi da kwayar Fara da kuma Shigari Kara 4.

” Wanda ya yi irin abunda na aikata hukuncinsa kisa ne, amma ni ban Shirya Mutuwa ba, Ina Neman afuwa ” Cewar Dan-Kuda “.

Yanzu haka dai yana Babban shashin gudanar da binciken manyan laifuka , na rundunar Yan sandan jahar Kano, don fadada bincike Kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *