INEC Ta Gargadi Wadanda Ba Su Da Katin Zabe Su Kauracewa Rumfunan Zaben Gwamnan Ondo

Spread the love

Hukumar zabe mai zaman kanta, ta kasa INEC ta gargadi mutanen da ba su da katin zabe na dindindin ( PVC) a zaben gwamnan jahar Ondo, da za a  gudanar,a ranar  16 ga watan Nuwamban 2024, karsu kusanci rumfunan zaben.

Kwamishinan zaben jahar, Prof. Kunle Ajayi, ne ya bayyana hakan a Akure babban birnin jahar Ondo, a jiya Talata lokacin da ake gabatar da adadin wadanda suka yi Rijistan zaben ga jam’iyun da za su shiga zaben gwamnan jahar.

Ajayi ya ce ya yi alkwarin cewa za su yi wa kowa adalci, kuma sahihin zaben .

Ya kara da cewa mutane miliyan biyu da dubu hamsin da uku da guda shida 2,053,006, ne suka cancanci kada kuri’unsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *