IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

Spread the love

Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN ta ce mambobinta sun cimma matsaya domin fara sayen man fetur daga matatar man Dangote kai-tsaye.

Shugaban ƙungiyar ta IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima, shi ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta.

Ya ce haɗin gwiwa da Dangote zai saka a samu wadataccen man fetur cikin sauki a faɗin ƙasar.

“Ina farin cikin sanar da cewa matatar Dangote ta amince ta fara sayar mana da man fetur da kuma dizel kai-tsaye domin rarrabawa a defo-defo ɗin mu da kuma sauran gidajen mai,” in ji Girima.

Ya buƙaci mambobin IPMAN ɗin da su mara wa matatar Dangote baya, inda ya ce hakan zai kuma farfaɗo da yanayin hada-hadar man fetur da kuma rage ƙarancinsa da ake samu a ƙasar.

Abubakar ya ce matakin zai kuma janyo bunƙasar ɓangaren man fetur ɗin Najeriya.

Matatar ta Dangote ta yi alkawarin fara sayar da man fetur ɗin ga mambobin IPMAN sama da 30,000 da kuma gidajen mai 150,000 a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *