IPOB: Najeriya na so a miƙa mata Simon Ekpa

Spread the love

Hedkwatar tsaron Najeriya ta nuna farin cikinta da kama Simon Ekpa wanda jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne a ƙasar Finland.

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ne ya bayyana hakan, bayan hukumomin Finland sun sanar da cika hannu da shi.

Cikin wani saƙo da kakakin ma’aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aike wa BBC ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista ekpa zuwa Najeriya don ya fuskanci shari’a.

A ranar Alhamsi ne hukumomin Finland suka kama Simon Ekpa tare da aika shi gidan yarin ƙasar, bayan gurfanar da shi a kotu, kan zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *