Iran ta naɗa sabon ministan harkokin waje bayan mutuwar Abdollahian

Spread the love

Majalisar ministoci ta Iran ta naɗa Mataimakin Ministan Harkokin Waje Ali Bagheri Kanias a matsayin muƙaddashin ministan harkokin waje bayan mutuwar Hossein Amir-Abdollahian.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an ɗauki matakin ne bayan ganawar da rassa uku na gwamnatin Iran suka yi – zartarwa, da majalisa, da ɓangaren shari’a.

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa na Ɗaya Mohammad Mokhber ne zai karɓi ragamar mulki a matsayin shugaban ƙasa.

Kundin mulkin Iran ya ce mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya zai yi mulki ne na tsawon kwana 50 idan shugaban ƙasa ya mutu.

Mokhber ya faɗa wa gidan talabijin na ƙasar cewa za su ci gaba da bin manufar Shugaba Raisi wajen “gudanar da ayyuka ba tare da wata matsala ba”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *