Iyalan yan sanda 88 da suka rasu sun karbi Chekin kudi sama da N40m a Kano.

Spread the love

Iyalan jami’an yan sanda 88 da suka rasa rayukansu a bakin aiki, a jahar Kano, sun karbi Chekin kudi naira Miliyan arba’in da dubu dari shida da sha takwas da sittin da takwas (40,618,068:17k).

Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, ASP Abdullahi Hussaini ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da Idongari.ng, a ranar litinin.

Yan sanda sun gurfanar da wani mutum bisa zargin yaudara da sace Adaidaita sahu a Kano

Sudan ta Kudu ta haramta giyar da ta hallaka dubban mutane

Da yake mika Chekin kudin kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, a madadin babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbekotun,  karkashin shirin kula da iyalan yan sandan , ya jinjina wa jami’an da suka kwanta dama, da irin gudunmawar da suka bayar a lokacin da suke bakin aiki.

CP Gumel ya ce ba za a taba manta wa da gudunmawa da kuma sadaukar da rayuwarsu domin kare kasarsu.

Sanawar ta kara da cewa, kwamishinan yan sandan ya shawarce su da su yi amfani da kudin yadda yakamata .

Kwamishinan yan sandan ya yi addu’ar samun rahma, tare da kira ga iyalan su ci gaba da yi mu su addu’a a koda yaushe.

A karshe wadanda suka ci gajiyar kudin bayyana farin cikin su, tare yin alkawarin yin amfani da kudin yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *