Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Shahuci Kano, ta dage sauraren da’awar shari’ar da iyayen yara da malaman Makarantar Imam Malik Bin Anas Littahafizul Qur’an Wat Tarbiyya Wat Ta’alim, dake unguwar Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso, kan karar da suka shigar da wasu mutane 8 , bisa zargin siyar da filin da tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayar a matsayin wakafi don gina makarantar isilamiya.
A zaman kotun na ranar Talata, lauyan masu kara barista Ahamed Makari, ya roki kotun ta ba su damar sanya sunan tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau , da kuma wadanda suka zama wajibi a sanya su, a kunshin shari’ar dan sadasu da sammaci a gajeren lokaci don su gabatar da da’awarsu.
Luyan da ke tsayawa wadanda aka karar, Barista Shehu Mai-Yaki, bai yi suka ba, kan rokon lauyan masu karar.
Alkalin kotun mai shari’a Mallam Muhammad Sani Ibrahim, ya amince da rokon.
Iyayen yaran da malamansu, sun cika harabar kotun don ganin yadda zata kasance a matsayinsu na masu kara.
- Hukumar alhazan Kano ta nuna damuwa kan rashin sayen kujerun aikin Hajjin bana
- Ba batun harajin Tinubu ba ne ya janyo ɗauke auren ‘yar Sanata Barau daga Kano’
Sai dai lauyansu Barista Ahmed Makari, ya ce ” ma su karar suna da damar zuwa kotun don sauraren shari’ar, kuma an ba wa kowa damar ya zo kallon shari’a.
Iyayen yaran sun shaidawa jaridar www.idongari.ng, cewa matukar suka rasa wannan makaranta karatun yayansu, zai shiga wani hali kasancewar anan suke samun ilimi.
A takaddar kyautar da filin mai kwanan watan 14 ga watan Augustan 2021, tsohon sanatan ya ce” Ni Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, na mallakawa makarantar Imam Malik Bin Anas Littahafizul Qur’an Wat Tarbiyya Wat Ta’alim, dake Sabuwar Gandu, Filoti mai lamba 44, layin mai unguwa a sabuwar Gandu karamar hukumar Kumbotso, a jahar Kano”.
Takaddar ta kara da cewa,” na sadaukar da wannan fili ga wannan makaranta a matsayin wakafi, domin habaka ilimin addinin musulinci don haka ba za a shigar da wannan fili, a cikin dukiyar gado ba, kunma ba za a yi amfani da shi don kasuwanci ko wani dalili daban ba.
A karshe ya ce ” Rabbana Takabbal Minna , ya sanya sunansa da kuma sanya hannu”.
A bangaren lauyan wadanda aka yi kara Barista Shehu Mai-yaki, ya ce ba zai yi magana da manema labarai ba har sai ya nemi izini daga na sama dashi.