Jagororin majalisar wakilan Najeriya sun ziyarci matatar mai ta Dangote

Spread the love

Shugabannin majalisar wakilan Najeriya sun ziyarci matatar man fetur da hamshaƙin ɗan kasuwar ƙasar, Alhaji Aliko Ɗangote ya gina a birnin Legas.

Cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Hon. Tajudeen Abbas ya wallafa shafinsa na X – wanda kuma shi ne ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar -ya ce sun tattauna batutuwa masu amfani da shugaban matatar Alhaji Aliko Dangote.

Ziyarar ‘yan majalisar ita ce ta biyu zuwa matatar cikin wata biyu.

Baya ga kakakin majalisar, akwai kuma mataimakinsa, Hon. benjamin Kalu da Hon. Ikenga Ugochinyere a cikin tawagar

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matatar ke shirin fara fitar da mai a wata mai zuwa, yayain da yake fuskantar matsalar samun ɗanyen man da yake buƙatar tacewa daga kamfanonin mai na duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *