Jajirtattun yan sandan Kano 14 sun samu karin girma daga SP zuwa CSP

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Moluhammed Usaini Gumel, ya yi wa wasu manyan jami’an rundunar yan sandan jahar 14 , adon Karin girma sannan ya yi wa jami’an Lacca.

Sabbin Jami’an da aka yi wa Karin girman sun samu shaidar tantance wa daga Hukumar Kula da aiyukan Yan Sanda (PSC) ta fitar a ranar 15 ga Fabrairu, 2024, bisa shawarar baban Sufeto-Janar na yan sandan Nigeria.

Gumel ya umurci jami’an Yan sandan da kuma sabbin jami’an da aka Karawa girman su kara jajirce wq, wajen rubanya kokarin su, domin karin girma ya kan zo ne tare da karin nauyi.

“Wannan karin girman nuni ne na jajircewar Jami’an da suka sadaukar da kai ga ayyukan su.”

Yan sandan Kano sun cafke Mutane 178 cikin watanni 2 bisa zargin aikata laifuka maban-banta

A jawabin shi na godiya a madadin sabbin jami’an da aka karawa girman, jami’in da ke kula da sashin shari’a da kuma masu gabatar da kara na rundunar yan sandan, CSP Ekwe Sunday Osogu da aka yi wa ado ya bayyana cewa, salon jagorancin CP ne ke baiwa jami’an kwarin gwiwa, su sadaukar da kan su don samun karin girma yayin da suka yi alkawarin tabbatar da kwarewa da kuma bin doka da oda wajen gudanar da ayyukan su.”

 

 

 

 

 

Gajerin sunayen jami’an da aka karawa girma daga SP zuwa CSP.

1. Ekwe Sunday Osogu
2. Umar Auwal
3. Chika Abubakar Zaki
4. Mohammed Alhaji Mohammed
5. Muhammad Dauda
6. Tanimu Wada
7. Mahmoud Murtala Mahmoud
8. Aliyu Musa Salisu
9. Kaigama Ahmed Shuaibu
10. Dahiru Aliyu Madawaki
1. Alhassan Isyaku
12. Ibrahim Mudassir
13. Sani Garba
14. Ibrahim Garba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *