JAMA’A NAJERIYA FA NA CIKIN MATSALA WLLH YA KAMATA MU FARKA DA WURI..

Spread the love

Adaidai wannan lokaci Najeriya ta shiga cikin tsaka Mai Wuya sakamakon Mummunan TUKIN TSAYE( TUKIN GANGANCI) da ake wa Jama’ar Kasar..

Lamarin kullum kara taazzara yake a ‘Yan shekarun nan tsadar rayuwa, tsadar kayan abinci, tsadar Lafiya, tsadar Ilmi, rashin ruwa da Wutar lantarki, masifu iri iri kullum kara bullo suke sakamakon rashin iya shugabanci na gwamnatin Kasar.

An fuskanci mugun dagawar farashin kayan Abinci da kaso 150 cikin 100 duk Abinda ake saida shi naira 50 a da yanxu 200 ne koma 250, hakan yasa daruruwan Mutane basacin Abinci sai biyu a Rana bama a maganar aci Abu Mai gina Jiki.

Yanxu Kuma an shiga wani yanayi da ba’a taba ganin irinsa ba da litar man fetur Wanda shine abin masarufi daya dake ragewa Al’umma tsadar Abubuwa yanxu Lita daya ta haura dalar amurka daya (1000) wasu wurarenma ta haura dubu dayan..

Kenan yanxu in kana sa mai a motarka ka Kai ‘Ya’Yan ka makaranta da ba nesa Sosai ba kullum zakasa Mai Akalla na dubu 5 galan daya ka kaisu ka dakko su shikenan ya Kare, a sati zakasha man dubu 25 kenan a wata zakasha mai na dubu 100 sati hudu..

In Kuma kace su hau commercial suje, baka da tabbacin tsaro, km Shima ga tsada ga Kuma karancin ababen hawan a Kan hanya sakamakon wahala da tsadar man, sai yaranka su rinka makara km su rinka dawowa a wahale.

Har yanxu samun mutanen Kasar bai karuba Amma kashewarsu da bukatunmu Sun karu da Kashi 100 cikin dari..

Anya haka za’a cigaba da zama kenan.
Wannan itace Demokradiyyar tamu.
To Yakamata kowa ya fara tunanin abinyi daga yanxu inba haka ba wllh kasar zata hargitse domin mutane zasu fara mutuwa a tsaye ko a tafe sbd matsi da wahala da talauci da wasu tsiraru suka samu su kuma sunata satar dukiyar kasar suna siyan kadarori da boyewa a bankuna..

Allah ya kawowa talakan Najeriya dauki, Amma ya kamata mu fara tunanin abinyi..

Fatihu Yusuf
30/4/2024

#nigerianarecryingandonhardship#
#PresTinubuassistchangetheleadershipstyle#

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *