Jama’ar Garin Sheka Ku zauna lafiya, kar Abun da ya faru ya zama tashin hankali: Dagacin Sheka.

Spread the love
Dagacin Sheka Alhaji Abubakar Musa Zakari.

Dagacin garin Sheka a karamar hukumar Kumbotso Kano, Alhaji Abubakar Musa Zakari , ya hakurkurtar da mutanen yankin bisa wani abu da ya faru mara dadi na rasuwar wani matashi da yammacin jiya Lahadi.

Jaridar idongari.ng, ta ziyarci Unguwar da lamarin ya faru, inda shaidun gani da ido suka bayyana cewa, wani mutum ne mai suna Mallam Muhammad Sheka, ne ya shigar da korafin sa, wajen jami’an yan sanda da cewar Ana fada wa dansa suna mara dadi ( Kwalo) shi kuma baya so.

Sun Kara da cewa, bayan jami’an yan sandan sun zo Ana zargin sun Yi amfani hayaki mai sa hawaye sakamakon hayaniyar da ta kaure a makotan layin da abun ya faru sakamakon fadin sunan tsokanar Kwalo da ake fadawa dansa.

Tunda fari dai Wanda ya Yi korafin sun rabu da matar, Wanda hakan yakai Su har gaban kotu, don abashi damar rike yayan da Suka haifa guda uku, amma riciki ya kaure tsakanin sa da sirikinsa.

Daga cikin yaran ne ake zargin sun shaida wa mahaifin na su cewar , an fada wa Daya daga cikin su sunan Kwalo.

Dagacin shekar Alhaji Abubakar Musa, ya kara da cewa, bayan abun ya faru , ya zo da kansa domin gani tare da kokarin an hakurkurtar da iyayen mamacin bayan hatsaniyar da faru bisa yunkurin kone ofishin Yan sandan sheka da wasu batagarin Matasa Suka Yi.

Ya ce tuni suka gana da baturen Yan sandan Sheka, da kuma mukaddashin Kwamishinan Yan jahar Kano, Kan lamarin wadanda Suka Yi mu Su alkawarin bin tsarin Shari’a .

” Insha Allah wadanda Suka Yi wannan Abu za a duba aga maye tsarin da Suka Yi , ta wacce hanya Suka bi haka ta faru “.

Dagacin ya ce tuni ya bayyana wa iyayen mamacin alkawarin da rundunar Yan sandan jahar Kano, ta Yi domin ganin anbi hakkin Wanda Allah ya Yi wa rasuwar.

Sai da muka rika sayar da kwandon tumatur 1,000 saboda rufe boda’

Gwamnan Oyo Ya Rufe Kamfanin Hakar Ma’adinan ’Yan China

Sai dai ya Kara da cewa bisa labarin da ya samu , shi ne anzo gayyatar wani da ake zargi da aikata laifi , kuma dalilin haka ne ya haifar da wannan abu.

” ba da bindiga ba ne , muna tunanin kamar zuciyarsa ce ta buga don akwai hotuna, duk an dauka naga kirginsa kamar abun Tiyagas ne ya daki kirginsa” Dagacin Sheka”.

Mahaifin Isma’ila Inusa Yakubu mai suna Inusa Yakubu, ya bayyana cewa lokacin da zai tafi aiki saida mamacin ya ce masa Baba adawo lafiya, kuma tsakanin sa dashi sai son barka.

Mallam Inusa Yakubu mahaifin marigayi Sama’ila Inusa

Ana ta bangaren mahaifiyar mamacin Halima Inusa , ta ce , riciki ne ya faru tsakanin wasu surikai bayan an cewa dansa Kwalo, inda fada ya kaure har sai da yan unguwa suka raba su.

Inda shi kuma Malam Muhammed ya yi kira wo jami’an Yan sanda, har ake zargin sun harba barkonon tsuwa, kuma ana kautata zaton shi ne, ya yi sanadiyar rasuwar Sama’ila bayan an kaishi Asibitin Mallam Aminu Kano.

” Allah ya ji kansa shi bada shi ake fadan ba, abi mana hakkin mu, domin bashi da abokin fada” Halima” .

A karshe Dagacin ya Yi kira ga al’ummar garin sheka da a zauna lafiya abarwa shari’a ta yi aikin ta.

Kawo yanzu dai rundunar yan sandan jahar Kano , ta ce ta Fara gudanar da bincike kan faruwar lamarin kuma zata bayyana wa al’umma halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *