Jami’an hukumar tsaron Civil Defense reshen karamar hukumar Ungoggo Kano, sun samu nasarar cafke wani tsoho mai suna Ibarhim Usman mai shekaru 85 a duniya bisa zarginsa da aikata laifin garkuwa da wani karamin yaro mai shekaru 3 a duniya/Wanda dan makocinsa ne domin karbar kudin fansa.
- Kakakin hukumar tsaron civil defense na jahar Kano Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari. ng, a jiya Alhamis.
Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano, majalissar dokoki kan nada Kantomomi
Ya ce mutumin ya Yi garkuwa da Yaron ne a yankin Unguwar Riminkebe karamar hukumar Ungoggo ,inda yake kokarin boye yaron a Hotoro a gidan wani abokinsa.
Rahotanni na cewa, Wanda ake zargin ya yaudari Yaron da Alewa , har ya dauko shi a cikin baburin Adaidaita sahu, sai dai Abokin nasa yaki karbar yaron.
Bayan haka Abokin nasa ya tafi da yaron zuwa Unguwar Riminkebe, kuma ya samu dandazon jama’a suna ta kokarin ganin yadda za a samu Yaron.
Koda a watanni biyu da suka gabata dattijon da ake zargi ya taba Karbar nambar mahaifin Yaron, amma bai taba kiransa ba.
Wasu dai sun shaida hukumomin tsaron cewar an ga dattijon da Yaron amma dai ya musanta zargin.
A karshe kakakin hukumar tsaron civil defense din Ibrahim Idris , ya ce yanzu haka sun Fara fadada bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.