Jami’an Civil Defense Sun Bude Wuta A Jos

Spread the love

Mazauna garin Jos sun shiga cikin zullumi bayan da jami’an Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) suka yi ta harbe-harbe a ranar Asabar.

Jami’an na Sibil Difens da ke aiki karkashi Hukumar Kula da Ci-gaban Garin Jos (JMDB) sun bude wuta ne a yayin wani samame da suka kai katafare shagon sayar da kayayyaki na S.O Plaza, lamarin da ya haifar da rikici.

Jami’an hukumar sun kuma lakada wa wani matashi mai aiki a plazar duka, lamarin da ya rincabe zuwa tayar da jijiyoyin wuya.

A yayin samamen, jami’an tsaron sun ce sun je ne domin kama wata babbar mota da ta keta dokar  hana manyan motoci shiga garin.

Amma wani bidiyo da ke yawo ya nuna cewa an ajiye motar ce a cikin harabar plazar kuma ba ta tare hanya ba.

Mazauna garin Jos sun bayyana cewa ba jami’an da ke aiki da JMDB sun yi kaurin suna wajen yin irin haka, inda suke lalata dukiyar jama’a a yayin samamen da suk kaiwa tare da nuna karfin makamai, da ke jefa jama’a cikin firgici.

Mamallakin S.O Plaza, Mista Solomon Okeke, the owner of S.O Plaza, ya bayyana abin a matsayin barna.

Ya kara da cewa ko a watan Agustan bara, wani Manajan Hukumar JMDB, Hart Bankat, ya jagoranci jami’an Sibil Difens zuwa plazar ya sa suka harbe tayoyi shida na wata babbar mota a cikin harabar wurin, wanda ya jawo musu asarar miliyoyin kudade.

Mista Okeke ya bayyana cewa jami’an “sun yi awon gaba da wata babbar mota cike da kaya, kuma sun yi wa wani dan shekara 19 duka suka yayyaga masa kaya, kuma har yanzu ba a san inda yak ba.

“Me ya sa duk lokacin da suka zo sai sun yi ta harbe-harbe suna dukan ma’aikata sun lalata dukiyar jama’a?”

A nasu bangaren, mazauna yakin na Bukuru sun bukaci Gwamna Caleb Mutfwang ya sanya baki tare da taka wa jami’an JMDB burki kan irin yadda suke wuce gona da iri domin a samu zaman lafiya.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Janar Manajan JMDB, Akitet Hart Bankat, amma har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton haka bai samu ba, saboda jami’in bai ba da amsa ga tambayar da aka yi masa ba.

AMINIYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *