Jami’an DSS Sun Yi Kunnen Kashi Da Umarnin Alkali Kan Hana Su Yin Kame A Harabar Kotu

Spread the love

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun yi watsi da gargadin alkali inda suka kai samame harabar Babbar Kotun Jihar Ogun, inda suka kama wasu mutane biyu da ake tuhuma.

Da farko alkalin kotun, A.A. Shobayo, ya hana jami’an kama wadanda suke nema a harabar, su bari sai sun fito amma jam’an suka ki, lamarin da ya ja mu su Allah wadai.

A shari’ar wadda wani mai suna Cif Akeem Adigun ya shigar, yana zargin Alhaji Isiaka Fatai, Samuel Oyero da wasu mutane 12 da laifin kone  dukiyar al’umma.

A baya-bayan nan ne rikicin sarauta ya barke a garin Agosasa da ke karamar hukumar Ipokia ta jihar, inda aka yi asarar rai da dukiyoyi na biliyoyin Naira.

A sanarwa da ya fitar, Kehinde Bamiwola, lauyan Alhaji Isiaka, ya zargi jami’an DSS din da yi amfani da makamai kan wadanda ake zargin, inda ya jaddada cewa “an yi wa Alhaji Isiaka dukan tsiya, an kuma ci zarafinsa.”

Babban magatakardar kotun, Kwamared Omololu Olusanya, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro da rashin mutunta doka.

Ya ci gaba da cewa, alkalin kotun ya umarci jami’an kada su kama su a harabar kotun, amma suka ki.

“A garin wannan aika-aika suka ci zarafin wata ma’aikaciyarmu; wannan abin bakin ciki ne da ya haifar da hayaniya mai yawa a harabar kotun.

“Majiyarmu ce ta sanar da mu cewa jami’an DSS ne, amma idan wani ya gan su, zai zaci ’yan fashi da makami ne.

“Ba su sanya wani abu da ya bayyana su a matsayin DSS ba, amma sun zo wurin alkali da safiyar nan suka ce suna da wasu da za su kama. A lokacin ne muka san su jami’an DSS ne.

“Sun tunkari alkalin kotun kafin a fara zaman kotun, ya shawarce su da cewa idan har ana son a kama su, to kada a yi hakan a harabar kotun.

“Suna iya zama a waje su yi duk abin da suka ga dama, amma suka ki wannan shawarar suka yi kamen a cikin harabar,” in ji shi.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, bai amsa kira ko sakon tes da aka aika masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *