Jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka,FBI, wadanda suka gudanar da bincike a kan tuhumar da aka yi wa Shugaba Donald Trump,tuhumar da aka yi watsi da ita yanzu suna fuskantar kora daga aiki a wani mataki na yin garambawul a hukumar.
Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa gomman jami’an hukumar ta FBI da suke da hannu a binciken magoya bayan Trump ma da suka yi tarzoma da kutse a ginin majalisar dokoki kasar, Capitol, ranar 6 ga watan Janairun 2021 su ma suna fuskantar raba su da aiki.
Jaridar Washington Post ta ce ko a ranar Litinin an kori wasu jami’an ma’aikatar shari’a ta Amurka da suka yi aikin shari’ar magoya bayan Trump kan tarzomar ginin majalisar.
Jaridar ta ruwaito cewa an kori jami’an ne saboda mai rikon mumakin babban lauyan gwamnati, James McHenry, na ganin ba za su da ce da aiwatar da manufofin Trump ba.
Ita ma kafar CNN ta ruwaito cewa akalla manyan jami’an FBI shida aka bai wa umarnin ko dai su yi ritaya ko su sauka daga aiki ko kuma a kore su zuwa jibi Litinin.
Sanata Dick Durbin, babban dan majalisar dattawa na jam’iyyar Democrat, wanda ke kwamitin kula da harkokin shari’a, ya yi kakkausar suka a kan korar.