Jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya sun ce sun kama Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Bobriksy ne a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa daga Najeriya a iyakar Seme.
“Muna son mu sanar da al’umma cewa mun kama Idris saboda abubuwa da suka faru a baya-bayan nan. Yana ci gaba da amsa tambayoyi kuma za mu miƙa shi ga hukumomin da suka kamata domin ɗaukar mataki,” in ji hukumar.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen tsare kan iyakokin Najeriya yadda ya kamata.