Jami’an Tsaro Da Fursunoni Sun Mutu A Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yarin Mogadishu

Spread the love

Mutum takwas sun mutu bayan arangama tsakanin fursunoni da jami’an tsaro a gidan yarin Mogadishu

Jami’an tsaron Somaliya sun ce wasu fursunoni biyar da ake zargin ‘yan ƙungiyar Al-Shabab da masu gadi uku sun mutu sakamakon wata arangama tsakanin fursunonin da jami’an tsaro, bayan yunƙuri na tserewar fursunoni daga babban gidan yarin Mogadishu.

Akwai wasu rahotanni da ke zargin shigar da gurneti da bindigogi cikin inda ake tsare da fursunonin.

Rahotonni sun ce an fara gwabza ƙazamin faɗa ta hanyar tayar da manyan bama-bamai, sannan daga bisani aka fara harba bindigogi tsakanin jami’an tsaron gidan yarin da fursunonin da ke ɗauke da makamai.

Wani jami’in gidan yarin ya ce wasu ƙarin fursunoni 18 da sojoji uku sun jikkata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *