Jami’an tsaro sun yi wa majalisar dokokin Cross River tsinke bayan tsige kakakinta

Spread the love

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da na ‘yan sanda a Najeriya sun yi wa harabar zauren majalisar dokokin jihar Cross River ƙawanya, inda suka ƙwace iko da majalisar.

Matakin na zuwa ne bayan majalisar ta sanar da tsige kakakinta, Honarabul Elvert Anyambem a yau Laraba da rana.

Rahotonni daga ƙasar na cewa ‘yan majalisar dokokin jihar sun tsige kakakin nasu ne saboda zargin ɓarnatar da kuɗi da suke yi masa.

‘Yan majalisar sun kwashe watanni suka yunƙurin tsige kakakin nasu sakamakon abin da suka kira ”rashin gamsuwa da tsarin jagorancinsa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *