Wasu Jajirtattun jami’an rundunar yan sandan jahar Kano su 63, sun sami karin girma daga matakin, Deputy Superintendent of Police ( DSP) zuwa Superintendent Of Police ( SP).
Bikin karin girman ya gudana ne a jiya Litinin, bayan samun shaidar tantancewa daga hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa ( PSC) dangane da jajircewar su, wajen kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, sannan kuma ba a taba samun su da aikata wani laifi ba.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa karin girman ana ba wa , wadanda ba a taba samun da aikata laifi ba kamar yadda jaridar idonagri.ng, ta ruwaito.
” Kuma wadannan dukkansu yan sanda ne na jahar Kano, kuma cikin shekarun da suka yi, suna aiki ba a taba samun su da laifi ba” CP Gumel”.
CP Gumel, ya kara da cewa, sakamakon tantancewar hukumar kula da aiyukan yan sanda, ta tabbatar da cewar sun cika duk ka’idojin samun karin girman.
Ya kuma ja hankalin yan baya da suka kara jajircewa kan aiyukansu, don kar su bari wani laifi ya shiga cikin bayanan su na daukar aiki, da kuma rashin nuna hazaka a aiyukansu.
Kwamishinan ya karfafi gwiwar wadanda Allah ya ba wa karin girman , su kara jajircewa don samun karin girma na gaba.
” Idan kuka bi a hankali, kuka yi hakuri wata rana wasun ku su, za su zama kwamishinan yan sanda, Mukaddashin sufeton yan sandan Nigeria , ko ma IGP , amma sai da hakuri” CP Gumel”.
Kotu ta ƙi amincewa da belin Nnamdi Kanu
Kotu ta kori ƙarar lauyan Nnamdi Kanu kan ‘yan sanda da DSS
Wasu daga cikin wadanda suka sami karin girman sun hada da, SP Salahuddin I Dalhatu, SP Muhammed Alkasim, SP Sani Dan-Madugu da dai sauransu.
Guda daga cikin jajirtattun yan sandan 63, da suka sami karin girman, SP Salahuddin I Dalhatu, ya godewa Allah madaukin sarki da wannan ni’ima da suka samu a madadin sauran abokan aikinsa.
Ya kuma godewa hukumar kula da aiyukan yan sanda , babban sufeton yan Nigeria, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, da kuma kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, bisa karfafa mu su gwiwa da yake yi akoda yaushe.
A karshe ya yi alkawarin za su ci gaba da jajircewa wajen yin aiki, bisa kwarewa da kuma bin dokar aiki akoda yaushe.
Bikin karin girman ya samu halattar manyan jami’an yan sanda, yan uwa da abokan arziki, sarakunan gargajiya da dai sauransu.