Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya ce babu jami’insu da ya yi harbi lokacin zanga-zanga.
Sufeton ya yi wannan maganar ne a lokacin ya ke kare zargin da aka yi wa jami’ansu na yin harbi a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da ‘yan kasar ke yi.
Ya ce duk jami’in da aka gani da bakin kaya a ranar zanga-zanga ba jami’insu ba ne saboda ba kayan da suka saba sanyawa suka sa ba a ranar.
Sannan ya ce,sun kama masu dinka tutocin kasashen waje don su kai su wajen masu daukar nauyinsu.
A jihar Kano kuwa ‘yan sanda sun ce sun fara yi wa wadanda suka kama sharia.