Jami’ar Al-Istiqama Sumaila Ta Ba Wa NDLEA Tallafin Babura

Spread the love

Jami’ar Al-Istiqama Sumaila ta tallafawa Hukumar hana sha da Fataucin miyagun Kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano da Babura domin inganta aikin yaki da shaye-shaye.

Shugaban Jami’ar Farfesa Salisu Shehu ne ya mika Baburan guda biyu ga babbar Jami’ar Hukumar dake kula da Shiyyar Wudil, ACN Sadiya Ahmad Dogara a lokacin da suka kai masa ziyara a Ofishin sa.

Da yake Jawabi, Shugaban Jami’ar ya ce sun bada tallafin Baburan ne domin bada ta su gudunmawar, wajen kakkabe ayyukan ta’ammali da miyagun Kwayoyi a yankin domin samar da nagartacciyar al’umma.

A cewar Farfesa, “Na mika wannan tallafi ne a madadin mamallakin Jami’ar Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, domin tallafawa hukumar wajen gudanar da ayyukan ta na yau da kullum a yankin gaba-daya”.

A nata Jawabin, Babbar Jami’ar Hukumar dake kula da Shiyyar Wudil, ACN Sadiya Ahmad Dogara, ta ce sun kai ziyarar ne domin kara inganta alakar su da Jami’ar ta yadda za’a samar da tsarin wayar da Kan Dalibai dangane da illolin Shaye-shaye.

Sanarwar da Kakakin Hukumar na jihar Kano Sadiq Muhammad Maigatari ne ya aiko wa jaridar GTR Hausa, ta kuma godewa Jami’ar a bisa wannan tallafi da ta basu domin inganta ayyukan hukumar.

A karshe hukumar karkashin Jagorancin Babban Kwamandan ta na Kano Abubakar Idris Ahmad, ta bada tabbacin fatattakar harkar ta’ammali da kayan maye a cikin Jami’ar, yankin karamar hukumar Sumaila dama Shiyyar ta Wudil gaba-daya.

GTRHAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *