Cibiyar binciken noma a yankuna masu ƙamfan ruwan sama ta jami’ar Bayero a jihar Kano BUK, a Najeriya da kuma Jami’ar Reading da ke Burtaniya, sun ƙirƙiro garin dawan da zai ɗauki dogon lokaci bai lalace ba.
Haɗin guiwar ya kai ga ƙirƙiro hanyar ƙunshe garin dawan da waken soya da suka ce zai ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da ya lalace ba.
Cibiyar ta ce bayan shafe tsawon lokaci suna gudanar da bincike da hadin gwiwar cibiyar ICRISAT da kuma wani kamfani, a yanzu an samar da garin dawar wanda za a iya tuka tuwo da shi ba tare da ɗanɗanonsa ya sauya ba.
Garin dawa na daga cikin garin hatsin da mutane da yawa ke amfani da su wajen yin tuwo, musamman a arewacin Najeriya.
Masoya tuwo za su yi fatan ƙirƙiran garin ba zai tsaya kawai a kan dawa ba, musamman yadda farashin abinci ke ƙara hauhawa, lamarin da ke buƙatar alkinta wanda ake da shi.