Jami’ar Khalifa Isiyaka Rabi’u, Ta Yaba Wa Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano

Spread the love

Shugaban jami’ar Khalifa Isiyaka Rabi’u, Farfesa Abdurrashid Garba, ya bayyana gamsuwarsa da irin dauwamammen zaman lafiyar da jami’ar, ta samu tunda Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya Kama aiki a jahar.

Shugaban jami’ar, ya bayyana haka ne a ziyarar godiya, da ya Kai wa Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, a ofishinsa da ke Unguwar Bompai a ranar Laraba.

Farfesa Garba, ya yi alkawarin ci gaba da, bayar da goyon baya ga rundunar Yan sandan, don cimma burin da ake fata na tabbatar da tsaro a jahar.

Da yake nasa jawabin Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana muhimmancin da jami’ar ta ke da shi a cikin al’umma , inda ya tabbatar da cewa jahar Kano ce wadda tafi kowacce jaha a fadin Nigeria zaman lafiya.

CP Gumel, ya kuma bayyana irin kokarin da rundunar Yan sandan ke yi wajen kakkabe aiyukan batagari dake jahar, bisa goyon baya da hadin kan da al’umma da ke ba su a koda yaushe.

A karshe Farfesa Abdurrashid Garba, ya godewa kwamitin zartarwar jami’ar, bisa damar da Suka bayar wajen Kai ziyarar ga Kwamishinan Yan sandan.

Shugaban jami’ar, ya samu rakiyar wasu daga cikin ma’aikatan jami’ar, wadanda Suka bayyana Farin cikinsu da tare bayar da hadin Kai da goyon baya , a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *