Jam’iyar ADC Za Ta Dauki Matakin Shari’a Kan Hukumar Zaben Kano.

Spread the love
ADC

Shugabannin jamiyyar ADC a kananan hukumomi 44 na Jihar Kano, sun ce za su dauki matakin shari’a kan hukumar zaben jihar Kano saboda sanya kudin siyan form din takara da ya shallake hankali, Form din takarar shugabannin karamar hukuma Naira Miliyan 10, sai Naira Miliyan 5 ga dan takarar Kansila.

Hakan na kunshe ne a bayanin bayan taro da shugabannin suka fitar a ayau Asabar, inda shugabannin Jamiyyar sun ce matakin hukumar zaben Kano karan tsaye ne ga kudirin shugaban kasa da kuma hukuncin kotun koli da ta bai wa kanan hukumomin cikakken iko.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran Jamiyyar a karamar hukumar Taruni Comrade Aliyu Hydar ya fitar a madadin sauran shugabbanin jamiyyar, ta bayyana cewa kudurin ya samu goyan bayan kafatanin shugannin jam’iyyar na kananan hukumomi.

Sai dai Jamiyyar ta shawarci sauran Jamiyyu da kada su yi kasa a gwiwa ko kuma jikinsu ya yi sanyi wajen shiga a dama da su a wannan zabe mai zuwa da za a yi a ranar 30 ga Nuwamban 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *