APP ta lashe ƙananan hukumomi 22 daga cikin 23 na jihar Rivers

Spread the love

Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 22 cikin 23 na jihar Rivers da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na jihar (RSIEC), Adolphus Enebeli ne ya bayyana sakamakon ranar Asabar da daddare a Fatakwal, babban birnin jihar.

Haka kuma, hukumar zaɓen ta dakatar da bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Etche, saboda a cewarta har lokacin ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar.

Shugaban na RSIEC ya kuma ce za a bayyana sakamakon zaɓen kansilolin duka mazaɓun jihar 319 tare da na shugaban ƙaramar hukumar Etche da zarar an kammala tattara sakamakon.

Tun da farko dai jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta ce ba za ta shiga zaɓen ba, sakamakon umarnin wata kotu da ta hana gudanar da zaɓen, kodayake gabanin zaɓen uwar jam’iyyar ta ƙasa ta yi kira ga ‘yan jam’iyyar su shiga zaɓukan.

Gwamnan jihar Siminalayi Fubara na takun-saƙa da tsohon gwamnan jihar, ministan Abuja Nyesom Wike, kan jagoirancin jam’iyyar PDP a jihar.

Rikicin nasu ya yi ƙamari ne lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar jihar, bayan da tsagin Wike ya samu a nasara kan tsagin Fubara, lamarin da ya sa magoya bayan Fubara suka fice daga PDP zuwa APP, inda suka yi takarar a can, shi kuwa Gwamna Fubara ya goyi bayansu.

Abin da masu sharhi ke kallon wani mataki ne na ficewar Fubara daga PDP, kodayake bai fitar da wata sanarwa a hukumance ta aniyar ficewa daga jam’iyyar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *