Jam’iyyar PDP ta mutu a fagen siyasar Najeriya – Kwankwaso

Spread the love

Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyar PDP mai hamayya a ƙasar ta mutu a fagen siyasar ƙasar.

Yayin da yake jawabi a ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Katsina ranar Asabar, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam’iyyar APC ta jefa kanta cikin abin da ya kira ”halaka”.

”Jam’iyyar PDP dama kowa ya sani a yanzu dai matacciya ce, dama mu ne a cikinta, kuma tun da ta saki layi, muka sake”, in Sanata Kwankwaso.

Ya kuma zargi jagororin gwamnatin APC da nuna halin ko- in-kula game da halin da ƙasar ke ciki, musamman ta fuskar matsalar rashin tsaro.

”Kuna gani yanzu idan kana son fita daga cikin Katsina, duk inda za ka bi, to tunani kake ta inda za ka bi”. in ji shi.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira ga talakawan Najeriya su kauce wa karɓar taliya ko wasu kuɗi da ya ce ba su taka kara suka karya ba a ranar zaɓe domin sarayar da haƙƙoƙinsu.

”Ku tabbatar cewa ba a sake kawo taliya mutane sun karɓa, sun je sun dafa, sun ci, sun kuma faɗa wahala na shekara huɗu su da ‘ya’ya da jikoki, kun dai ga duka wannan wahalar a kan talaka take ƙarewa,” in ji jagoran Kwankwasiyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *