Hon. Nasiru Bala Aminu Ja’o’ji ya ziyarci mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Ja’o’ji ya ziyarci mataimakin shugaban kasar ne a gidansa da ke fadar gwamnatin tarayya a Abuja.
A lokacin ziyarar sun tattauna abubuwa masu mahimmanci da su ka hada da ci-gaban jam’iyyar APC da na matasa a jihar Kano da kuma Arewacin Najeriya gaba daya.
Shettima ya yabawa Ja’o:ji kan irin gudunmawar da ya ke bawa jam’iyyar a jihar Kano da Kuma Arewacin Najeriya.
Shettima ya ce tabbas jam’iyyar na alfahari da matasa irinsu Ja’o’iji wadanda ke aiki tukuru dan bunkasa jam’iyyar.
Haka zalika Shettima ya ce jam’iyyar na sane da irin kabakin alkairi da Ja’o’ji ke yiwa matasa da mata a jihar Kano.
A lokacin da ya ke bayani, Ja’oji ya godewa mataimakin shugaban kasar kan tarbar da ya yi masa.
Ya kuma yi alkawarin ninka gudunmawar da ya ke bawa jam’iyyar ta hanyar bada tallafi ga matasa da mata kamar yadda ya saba.
A watan Disamba shekarar da ta gabata Ja’o’ji ya bawa matasa da mata tallafin miliyan 500 don su dogara da kansu.