Jaridari.ng, ta ba wa Alhaji Auwal Jos, hakuri sakamakon ambatarsa da ta yi a cikin Wani labarin da ta wallafa, Ranar Alhamis kan zargin siyan wata shinkafa.
Jaridar ta gano cewar Alhaji Auwal , ya bi dukkan matakan da yakamata, wajen siyan shinkafar, da Kungiyar ta samu daga gidauniyar Alhaji Aliko Dangote, karshin Hajiya Fatima Aliko Dangote,don raba wa Yayan Kungiyar Arewa online journalist dake cikin dandalin WhatsApp a makon jiya.
Wannan na zuwa ne sakamakon Wani bincike da jaridar ta sake yi , kan zargin siyan buhunan shinkafar guda 109, tare da tabbatar da cewa , Auwal ya siyi shinkafar a hannun kungiyar bisa ka’ida
- Gwamnatin Tarayya Ta Aiyana Ranakun Hutun Karamar Sallah
- Sojojin sun yi wa ‘yan bindiga kwantan ɓauna, sun kashe uku a Kaduna