Jawabin Mai Magana Da Yawun Gwamnan Jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Spread the love

Jawabin Mai Magana Da Yawun Gwamnan Jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Litinin, 5 ga Agusta, 2024

Assalamu Alaikum…..

Sakamakon abubuwan takaicin da ya faru a baya-bayan nan, inda wasu bata gari suka shiga rigar masu zanga-zangar lumana a Kano, inda suka yi ta barna da dukiyoyin gwamnati tare da al’umma masu zaman kansu, gami da raunatawa, tare da kashe ‘yan kasa daba su ji ba ba su gani ba a jihar Kano.

Mai girma Gwamna ya nuna bacin ransa tare rashin jin dadi ta yadda wasu ’yan siyasa marasa kishi suka yi amfani da wannan dama suka kawo hargitsi a jihar Kano domin kawai su cimma wani buri nasu na siyasa.

Gwamna yana mai bayyanawa karara cewa duk wanda aka samu da hannu wajen kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano za a yi maganinsa yadda ya kamata kamar yadda doka ta tanada yayin da gwamnati ke ci gaba da sanya ido sosai a kan lamarin.

Haka kuma gwamnati ba za ta dauki wani abu da wasa ba, don haka zamu ci gaba da yin taka-tsan-tsan kan al’amuran da suka shafi tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan al’umma.

Saboda haka gwamnati ta yanke shawarar sanar da jama’a abubuwa kamar haka:

1. A yau ne aka fara gurfanar da wasu mutane sama da 600 da ake zargin an dauki nauyinsu ne domin su kawo tarnaki a zanga-zangar lumana a Kano.

2. Gwamnan jihar Kano ya bayar da umarnin a dawo da cibiyoyi na koyon sana’o’i da cibiyoyi na horarwa, wadanda za’a dauki dubban matasan mu domin horar da su ilimin dogara da kansu.

3. An gyara tare da farfado da cibiyar gyaran hali taKiru kuma za a fara diban matasan da ke fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi domi a dawo da su hayyacinsu nan da wani lokaci.

4. Dangane da dimbin kiraye-kirayen da ’yan Najeriya masu kishin kasa, kasashen duniya, kungiyoyin kare hakkin dan Adam, kungiyoyin farar hula, shugabannin gargajiya da na addini suka yi gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa. domin a binciki kashe-kashe da barnata dukiyoyin gwamnati da na al’umma masu zaman kansu a jihar Kano.

5. Muna kira ga mutanen Kano masu albarka da su goyi bayan wannan matakai da muka dauka ta hanyar samar da bayanai masu amfani ga kwamitin binciken da za a sanar zai bukata.
6. Daga karshe muna so mu bayyana cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ba ta da alaka kai tsaye ko ta fakaice da duk wasu mutane masu zanga-zanga musamman masu rike da tutocin wata kasa.

Bissalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *