Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa jerin sunayen jakadu a kasashen waje da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta na karya ne.
Cikin wata sanarwa ma’aikatar ta bukaci jama’a su yi watsi da jerin inda ta ce shugaban kasa ne kadai zai iya nada jakadun Najeriya a kasashen waje.
“Nada jakadun kasar waje, hurumin shugaban kasa ne kadai, kuma bai nada kowa ba,” in ji sanarwar.
Sanarwar wacce mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje Komiebi Ebienfa, ya sanyawa hannu ta ce al’ummar Najeriya kada su dauki jerin da mahimmanci.