Jigawa ta fi kowace jiha tsadar man fetur a watan Mayu

Spread the love

Farashin litar man fetur ɗaya ya kai naira 937.50 a jihar Jigawa da ke arewacin ƙasar a watan Mayun da ya gabata, in ji hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS.

Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa farashin da kwastomomi suka biya a Jigawa shi ne mafi tsada a faɗin ƙasar, abin da ke nuna ƙaruwar farashin tun bayan cire tallafi shekara ɗaya da ta wuce.

Rahoton ya kuma ce farashi na tsakatsaki da mazauna jihar suka biya a kan litar fetur ɗin shi ne N769.62, wanda ke nufin ƙarin kashi 223.21 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin (N238.11) da aka sayi man a watan Mayun 2023.

Idan aka kwatanta da farashin watan Afrilun 2024 kuma, an samu ƙarin kashi 9.75 ne cikin 100 (N701.24).

Jigawa ce ta fi kowace jiha tsadar fetur ɗin a Najeriya, inda ake sayen lita ɗaya kan N937.50, sai kuma jihohin Ondo da Binuwai masu N882.22 a watan na Mayu.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da sanawar cire tallafin ne a jawabin da ya gabatar na ranar 29 ga watan Mayun 2023 yayin shan rantsuwar kama aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *