Jihar Sokoto na horar da ɗalibai mata 151 don rubuta jarrabawar shiga jami’a

Spread the love

Asusun raya limi na jihar Sokoto ya zaɓi ɗalibai mata 151 daga makarantu daban-daban na jihar, inda yake ba su horo kan yadda za su rubuta jarrabawar shiga jami’a, mai zuwa.

Shirin wanda kwamishinan ilimi matakin farko da kuma sakanadire na jihar, Mohammad Tukur Alkali, ya ƙaddamar na da nufin bai wa matasan mata ilimi da ƙwarewar da za su iya yin fice a fannin ilimi.

Matsaloli da dama na zama kalubale ga burin ‘ya’yan mata na samun karatu na Najeriya.

Matsalolin kwa sun haɗa da talauci, wanda ke sa iyaye fifita ilimin ‘ya’ya maza a kan na mata, inda ake yi wa matan aure suna da ƙananan shekaru saɓanin takwarorinsu maza.

Matsalar tsaro, na daga ƙalubalan da ke zama barazana ga ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar, inda ‘yanbindiga da sauran ‘yan ta’adda kan kai hari makarantu su yi garkuwa da ɗalibai musamman mata, kuma wannan na tsoratar da wasu iyayen kai ‘ya’yansu manyan makarantu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *