Jihohi 16 na neman Kotun Koli ta hana EFCC bincikar kudadensu

Spread the love

Kotun koli ta sanya 22 ga watan Oktoba 2024 a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da jihohi suka shigar gabanta na neman hana hukumomin yaki da almundahana bincikar asusun ajiyarsu.

Kwamitin alkalan kotun mai mutum bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Baba-aji ta sanya ranar ne bayan gwamnatiocin jihohi 16 sun shigar da karar neman ta hana Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon kasa (EFCC) da Hukumar Binciken Kudade ta kasa (NFIU) bincikar asusunsu.

“Muna neman kotun ta ayyana cewa EFCC ko NFIU ko wata hukumar Gwamnatin Tarayya ba su da ikon bincike ko neman bayanai ko gayyata ko tsare kowa saboda sha’anin kudaden jihohi ko kananan hukumomi,” kamar yadda yake kunshe a takardar karar da gwamnatin jihar Kogi take jagoranta.

Gwamnatin Kogi da sauran jihohi 15 na neman Kotun koli ta yanke hukunci, a shari’ar da ake karar Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a.

Hakan na zuwa ne a yayin da EFCC ke bincikar tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello kan zargin karkatar da Naira biliyan 110 daga asusun jihar. A watan Yuli ne Gwamna Usman Ododo ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar yaki da almundaha ta jihar.

‘EFCC haramtacciya hukuma ce’

Masu karar suna kalubalantar dokar da ta kamfa hukumar EFCC da cwea ta ci karo da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, don haka suke neman ta ayyana dokar a matsayin haramtacciya.

Jihohi 16 ne suka da suka shigar karar hadin gwiwar su ne  Kogi da Katsina da Sakkwato da Jigawa da Kebbi da Nasarawa da Neja da Filato da Binuwai da Anambra da Kuros Riba da Enugu da Edo Da Ogun da Oyo da Ondo.

Jihohin sun shaida wa kotun cewa a baya ta yanke hukunci cewa yarjejeniyar Majalisar dinkin Duniya Kan Yaki da Almundahana ce aka mayar dokar kafa hukumar EFCC.

Sun yi idirarin cewa Majalisar Dokoki ta kasa ba ta bi tanade-tanaden sashe ne 12 na kundin tsarin mulkin Nijeriya wajen yin dokar EFCC ta shekarar 2004, wanda kuma a cewarsu, wajibi ne yin hakan kafin yarjejeriyar ta zama doka a Nijeriya

Sashe na 12 na kundin tsarin mulkin ya ce, “(1) Duk wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da wata kasa ba za ta zama doka ba, har sai idan Majalisar Dokoki ta kasa ta mayar da ita doka.

“(2) Majalisar za ta yi dokar kasa ko ta wani yanki a kan duk wani lamari ba bai kebanci Gwamnatin Tarayya ba, domin aiwatar da yarjejeniyoyi.

“Ba za a gabatar wa shugaban kasa kudurin dokar da majalisar ta amince da shi a sashe na (2) na wannan sashen ba, har sai mafi rinjayen majalisun dokokin jihohi sun amince da shi.”

Don haka, jihohin suka shaida wa Kotun koli cewa, dole sai akasarin majalisun dokokin sun amince da kudurin amfani da yarjejeniyar yaki da almundahanar, kafin ma a yi dokar kafa hukumar EFCC.

Don haka, a cewarsu, babu yadda za a yi amfani da dokar EFCC da ake aiki da ita a yanzu a kan wata jiha, hasali ma, duk wata hukuma da dokar EFCC ta samar haramtacce shi.

Sannan babu yadda za a yi dokar ta EFCC ta yi aiki a jihohin da ba su amince da ita ba.

Saboda haka suke neman alkalan kotun kolin su ayyana cewa: “Gwamnatin Tarayya, ta hannun hukumar NFIU ko wata hukuma ba su da hurumin bayar da umarni ko duk wani abu makamancinsa game da gudanar da kudaden jihohi.

“Muna neman kotun ta ayyana cewa EFCC ko NFIU ko duk wata hukuma ko ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ba su da hurumin bincike ko neman bayani ko gayyata ko tsare kowa saboda abin da ya shafi kudaden jihohi ko kananan hukumomi.

Bayan sauraran su ne kotun koli ta ba da izini hade masu kara da korafe-korafen nasu, sannan mai Mai Shari’a Uwani Baba-aji ta dage zaman zuwa ranar 22 ga watan Oktoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *