Jihohi biyu ne kaɗai za su amfana da sabuwar dokar harajin Najeriya – Zulum

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnonin Arewa suka shawarci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ɗan dakata kafin ya tura daftarin dokar sake fasalin harajin ƙasar zuwa majalisar dokoki.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels ranar Lahadin da ta gabata, ya ce ƙungiyar gwamnonin Arewa na buƙatar lokaci ne domin tuntuɓa da kuma nazarin ɓangarorin dokar harajin.

“A kan wannan dokar, akwai abubuwa da dama da ba a fahimta ba. Mun duba tanadin da aka yi wa harajin VAT a cikin dokar. Bisa kididdigar da muka yi, Jihohin Legas da Ribas ne kaɗai za su ci gajiyar waɗannan sauye-sauyen. Mun yi namu binciken kuma mun gano cewa za mu yi asara,” inji Zulum.

“Me yasa muke hanzari? Mun shawarci Gwamnatin Tarayya da ta dakata, ta yi kakkaɓe wasu abubuwan da za su iya cutar da yankin Arewacin Najeriya.”

Zulum ya yi bayanin cewa idan har dokar ta sami amincewar Majalisar Dokoki ta kasa, za a cutar da jihohi da dama domin jihar Legas ce kaɗai za ta ci gajiyar wannan manufa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *