Jiran Tsammanin Shan Man Fetur Ya Janyo Rufe Titin Murtala Muhammed Kano.

Spread the love

Yayin da ake fuskantar tsadar Man Fetur da kuma Karancinsa a gidajen Mai , a fadin Nigeria, al’umma na ci gaba da kokawa kan yadda al’amura suka tsaya cik.

Rahotanni na cewa, a wasu sassan jahar Kano, gidajen man Fetur da dama suna Rufe, inda kadan daga ciki suka bude , amma ana siyarwa da tsada.

Tunda sanyin safiyar Talata , Masu ababen hawa suka kafa dogwayen layukan ababen hawa, don shan mai a sassan birnin Kano.

Jaridar idongari. ng, ta ruwaito cewa, yanzu haka kan Titin Murtala Muhammed Kano, an Rufe hannu daya sakamakon yadda Masu ababen hawa, suka sanya dogwayen layuka don shan man Fetur.

Rahotanni na cewa , Motaci, Adaidaita sahu da kuma Babura Masu kafa biyu sun haura 3500 , yayin da yan Bunburutu ke jiran tsammani da Jarkokinsu.

Jami’an hukumar Karota, ta Jahar Kano suna ta kokarin daidaito hanyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *