Jirgi ya yi ruwan bam a kan masu taron Mauludi a Kaduna

Spread the love

Ana ci gaba da nuna tsananin alhini, a lokacin da ake kokarin tantance yawan mutanen da suka mutu, a wani mummunan luguden wuta da jirgin sojin Najeriya ya kai kan wasu masu taron Mauludi a Tudun Biri cikin yankin karamar hukumar Igabi.

Wani shaida daga jihar ta Kaduna ya bayyana wa BBC cewa cikin tsakar dare ne wani jirgin sama ya jefa musu bam suna tsakiyar bikin Mauludi.

“Mun kuma je, muna son mu tsame wa’inda ba su cika ba, da ke neman taimako, to an fara jawo wa’inda suke da sauran rayuwa, kuma jirgin again ya kuma dawowa ya jefa bam din.”

Bello Shehu Ugara ya ce cikin wadanda suka mutu akwai mata da kananan yara har da na-goye.

“Da idona, na ga mutane kamar hamsin da aka kashe.”

A cewarsa, jirgin ya yi ta shawagi a kan mahalarta Mauludin kafin ya jefa musu bam a karon farko da misalin karfe 10 na dare.

Shaidan ya bayyana fargabar cewa mutanen da suka mutu sun kai gommai a iftila’in.

Rundunar sojin saman Najeriya tuni ta fitar da sanarwa, tana musanta duk wani hannu a wannan al’amari.

Sai dai, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar luguden bam din a kan “mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba”. Ta kuma bayyana shi da cewa abin takaici ne matuka.

Bello Ugara ya ce jirgin ye jefa bam din ne a daidai wata bishiyar mangwaro, inda suke halartar taron.

An kai mutum 30 da suka ji raunuka asibiti

Shaidan ya kara da cewa sun kai kimanin mutum 30 asibitin garin Buruku.

Ya ce suna Mauludin ne da sunan makarantar Madrasatul Madinatul Ahbab wa Talamiz da ke Ugara.

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Sojojin Najeriya sun sake gano wurin Ζ™era makamai a Plateau

Ya ce duk shekara sukan yi wannan taron Mauludi, kuma ko a kwanan baya sun yi wani makamancinsa, amma suka sake tsara gudanar da wani a daren Litinin.

A cikin wadanda suka mutu in ji Bello Ugara har da mata da yara “akwai matan aure wanda za ka ga matan ta mutu, jaririnta bai mutu ba. Akwai wanda za ka ga jaririn ya mutu, uwan ba ta mutu ba”.

“Akwai kuma yara kanana wadanda sun mutu, akwai matasa su ma sun mutu. Sannan akwai dalibai maza da mata, ba jinsin da bai mutu ba.”

irgin sojojin kasa ne – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta ce ta karbi bayanai game da lamarin da ya faru, wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata karin wasu.

Wata sanarwa da jami’i mai kula da ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida ta Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, ta ambato babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya, Manjo Janar VU Okoro na cewa dakarun sojin kasa ne a yayin wani aiki da suka saba, don kakkabe ‘yan ta’adda a yankin, amma cikin kuskure sai suka far wa taron mutanen gari.

A karshen taron wanda mataimakiyar gwamnan jihar ta jagoranta ya ambato Hadiza Sabuwa Balarabe tana mika sakon ta’aziyyar gwamnati da al’ummar Kaduna ga iyalan da suka rasa makusantansu.

Sanarwar ta ce har zuwa lokacin fitar da bayanin, ana ci gaba da kokarin nema da ceton mutanen da suka ji raunuka, yayin da gwamnati ta kai wasu asibitin koyarwa na Barau Dikko.

Dakarun tsaron Najeriya sun sha kai hari kan fararen hula da ba su ji, ba su gani ba a ayyukan da suke yi na murkushe ‘yan ta-da-kayar-baya da kuma Boko Haram.

A farkon wannen shekara ma, ‘yan sanda a jihar Nasarawa sun tabbatar da cewa mutum 28 ne aka yi wa jana’iza sakamakon wani luguden wuta da wani jirgin sojoji ya kai kan wasu rugagen Fulani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *