Jirgin Air Peace ya yi saukar gaggawa a Legas

Spread the love

Wani jirgin saman kamfanin Air Peace da ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

“Muna sanar da al’umma lamarin da ya faru da jirginmu da ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas ranar 25 ga watan Afrilu”.

“Mintuna kafin saukar, sai matuƙin jirgin ya fahimci wata alamar ƙarar gargaɗin wuta a inda direban ke zama. Direban ya yi ƙoƙarin ɗaukar duka matakan kariya, kodayake daga baya ƙarar ta daina”.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Direban ya yi gaggawar sanar da masu kula da filin jirgin na Legas, inda bayan saukar jirgin aka gano cewa ƙarar ta fara kaɗawa ne bisa kuskure, amma babu wata wuta da kama a jirgin”.

Jirgin – wanda ke ɗauke da fasinjoji 243 tare da ma’aikatan jirgin 12 – ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba.

Batun na zuwe ne kwanaki bayan jirgin kamfanin Dana Air ya zame daga kan hanyarsa a filin jirgin saman Legas, lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar da dakatar da kamfanin daga aiki, tare da ƙaddamar da bincike kan batun.

Saukar gaggawa da zamewar jirage daga kan titunansu dai wasu abubuwa ne da suka jima suna sanya fargaba a zukatan fasinjoji a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *