Jirgin Rasha ɗauke da mutum 22 ya ɓata a gabashin ƙasar

Spread the love

Wani jirgi mai saukar ungulu ɗauke da mutum 22 ya ɓata a tsibirin Kamchatka da ke gabashin Rasha.

Jirgin – wanda ke ɗauke da ‘yan yawon buɗe idanu – ya ɓace daga kan layinsa jim kaɗan bayan tashinsa daga yankin Vachkazhets mai ɗimbin tarihin dazukan namun daji.

Jami’an ƙasar sun ce rashin kyawun yanayi, ciki har da mummunan hazo na kawo tarnaƙi kan ƙoƙarin neman jirgin.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Al’amarin ɓacewar jirage ko faɗuwarsu na neman zama ruwan dare a yankin gabashin Rasha, mai cike da wuraren yawon buɗe idanu da kuma rashin kyawun yanayi.

Ko a shekaru uku da suka gabata ma sai da wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗi tare da kashe mutum takwas ciki har da ‘yan yawon buɗe idanu a yankin na tsibirin Kamchatka skamakon rashin kyawun yanayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *