Jirgin Sojin Nigeria Ya Yi Barin Wuta Kan Yan Sa Kai A Kauyen Tungar Kara A Jihar Zamfara

Spread the love

An samu rahotanni cewa ana ta ƙoƙarin kawar da gawarwaki, da kuma waɗanda suka tsira da munanan raunuka a garin Tungar Kara na yankin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, bayan da wani jirgin sama da ake zargin na sojoji ne ya kai ya yi kuren barin wuta kan wasu ƴan sa kai da jama’ar gari a yammacin Asabar.

An ce lamarin ya auku ne, yayin da ake ƙoƙarin daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai garin, suna ƙoƙarin kore wasu dabbobi.

Wani mutum, wanda ya rasa ɗan yayansa a wannan hari, ya bayyana cewa ƴan sa kai da dama ne lamarin ya rutsa da su yayin da suke yunƙurin tunkarar ƴan bindigan da aka ce suna ɓarna a yankin, inda ya kara da cewa ƴan bingidan sun riga sun bar yankin a lokacin da jirgin ya fara ɓarin wuta.

Ya ce: ”Muna zaune sai muka ga jirgi ya nufi wuraren da aka ce ƴan bindigan suke, amma ko a lokacin sun riga wuce. Waɗannan yaran da da mutanen da ke ƙasa ne wannan jirgin yake ta harbi, yanzu haka ga ɗan yaya na an kawo mun shi a mace.”

Ya ƙara da cewa aƙalla mutane 20 ne suka mutu sakamakon wannan hari.

jami’in watsa labarai na rundunar operation Fansar Yamma da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, inda ya ce zai bincika ya tuntuɓe mu. Haka shi ma mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya shaida mana.

Sai dai kuma wata majiyar gwamnatin jihar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa BBC aukuwar wannan lamari, amma bai yi wani cikakken bayani ba.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *