JNC Ta Bukaci Gwamnatocin Jahohi Da Tarayya Su Daidaita Tsarin Biyan Mafi Karancin Albashi Lokaci Daya.

Spread the love

Majalissar sasanta matsalolin ma’aikata da gwamnati JNC reshen Jihar Kano, ta bukaci jihohi da gwamnatin tarayya su daidaita tsarin mafi karancin albashin ma’aikata domin tabbatar da kammala aikin aiwatarwa aka lokaci, da baiwa ma’aikata damar samun sabon mafi karancin albashi cikin sauri.

A wata sanarwar manema labarai da aka fitar dauke da sahannun Mai magana da yawun JNC Comrade Magaji Inuwa, Shugaban Majalisar sasanta matsalolin ma’aikata da gwamnati, Kwamared Hashim A Saleh, ya yabawa gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago bisa amincewa da sabon mafi karancin albashi na kasa Naira dubu 70.

Saleh ya bukaci shugaban ma’aikata na Jihar Kano Abdullahi Musa da ya fara tattaunawa kan yarjejeniyoyin gwamnati da bangarorin kwadago domin aiwatarwa a matakin jiha.

Bugu da kari, JNC ta shawarci gwamnatoci da su bullo da tsare-tsare don dakile hauhawar farashin kayayyaki, domin tabbatar da mafi karancin albashin ma’aikata ya amfanesu.

A karshe ya yi kira ga ma’aikata da su sake sadaukar da kansu tare da marawa gwamnati baya wajen gudana da Nagartattun ayyukan hidimar al’umma.

Bugu da kari, Saleh ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ware naira biliyoyin Naira domin biyan kudaden gratutu na ma’aikata da suka yi ritaya daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *